Zaben raba gardama na yancin Montenegro | Labarai | DW | 21.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben raba gardama na yancin Montenegro

A yau jamaar Montenegro suke kada kuriar raba gardama,akan zabin yanci domin kawo karshen hadewarsu da Serbia.

Bincike dai ya nuna cewa,da kyar ne a samu kashi 55 cikin dari na kuriun amincewa da rabewa daga Serbia kamar yadda kungiyar taraiyar turai ta bukata.

Masu goyon bayan Serbia sun nuna cewa,akwai alaka mai muhimmanci tsakanin bangarorin biyu,amma masu goyon bayan yanci sunce janyewar Montenegro daga Serbia zai karfafa ci gabanta tare da gaggauta shigarta cikin kungiyar taraiyar turai.

Ba da jimawan nan bane dai kungiyar taraiyar turai ta dakatar da tattaunawa da Serbia game da batun shigarta kungiyar,saboda ta gagara tsare Ratko Mladic da ake nema da aikata laifukan yaki.