Zaben Najeriya: An samu tsaiko a Jihar Kano | Labarai | DW | 23.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben Najeriya: An samu tsaiko a Jihar Kano

Daga Jihar Kano dai zabuka na tafiya cikin kwanciyar hankali kuma tuni mutane da dama suka ka'da kuri'unsu ,sai dai kuma akwai tasoshin zabe da dama da suka sami matsalolin da ka kiya kawo tarnaki wajen kammala zaben.

Wakilinmu na Kano ya ce za a iya cewar tafiyar zaben babu yabo babu fallasa domin tuni ka'da kuriar zaben ya yi nisa a wasu mazabun sai dai wasu cibiyoyin zaben har wannan lokaci ba su sami kayan aikinsu ba na zabe, haka kuma wasu wuraren an kawo kayan aiki amma kuma katin tantance masu zabe wato card reader yana kawo tangarda wajen tantance masu zabe, lamarin da ya kawo tsaiko a wasu mazabun a Kano.