1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu tashin hankali a wasu Jihohin Najeriya

Abdourahamane Hassane
February 23, 2019

Kungiyoyin farar hula da ke saka ido a zaben, sun ce daga cikin Jihohin da aka samu tashin hankalin har da Jihar Legas inda aka hana wa wasu jama'ar jefa kuri'a, abin da ya sa wasu 'yan daba suka cinawa kuri'un wuta.

https://p.dw.com/p/3Dxri
Wata mazaba a Jalingo
Wata mazaba a JalingoHoto: DW/Isa Usman Jaalo

Hadin gwiwar wasu kungiyoyin farar hula masu saka ido a zaben Najeriya, sun ce an kashe mutane 16 a wasu Jihohi guda takwas na kasar, amma dai duk da haka zaben na ci gaba da gudana. Kungiyoyin sun ce daga cikin Jihohin da aka samu tashin hankalin har da Jihar Lagos inda aka hana wa wasu jama'ar jefa kui'a, abin da ya sa wasu 'yan daba suka cinawa kuri'un wuta. Haka ma a yankin kudu maso gabashin Najeriya a yankin Naija Delta an samu barkewar tashin hankali.