Zaben Gini Bissau ya gudana lami lafiya | Labarai | DW | 13.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben Gini Bissau ya gudana lami lafiya

Zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin kasar Gini Bissau ya gudana ba tare da an fuskanci tashin-tashina ba.

Al'ummar kasar Gini Bissau sun kada kuri'a a zabukan majalisun dokoki da na shugaban kasa, wadan ke zuwa shekaru biyu cif bayan da soji suka suka hambarar da gwamnatin wancan lokacin.

Vincent Foucher na kungiyar kasa da kasa ta sassanta rikici ta International Crisis Group na daya daga cikin wadanda suka sanya ido kan yadda zaben ya gudana, ya ce an yi komai cikin tasabta kuma ma kungiyoyi musamman ma kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka wato ECOWAS ta taka rawar gani wajen tabbatar komai ya gudana cikin kwanciyar hankali.

Tuni dai aka fara samun sakamakon zaben har labaran da muke samu ke cewe jamiyyar PAIGC ce take kan gaba yanzu.

A cikin makon gobe ne dai ake sa ran fitar kamalallen sakamakon zaben, sai dai za a iya tafiya zagaye na biyu na zaben in har ba a samu guda daga cikin 'yan takarar da ya samu gagarumin rinjaye.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Pinado Abdu Waba