Za′a mika sammaci ga Hama duk inda ya ke | Siyasa | DW | 29.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Za'a mika sammaci ga Hama duk inda ya ke

Al'ummar Jamhuriyar Nijar na ci gaba da dakon kotun tsarin mulki kan bukatar karar da Hama ya shigar a gaban kotu.Da ya ke bayani a gaban manema labarai Babban alkalin gwamnatin kasar
ta Niger wato Procureur de la Rep Malam Bukari Ibrahim Sally ya soma
ne da cewa ainihi dai ganin irin yadda hukumarsa ba ta da hurumin
sauraran shugaban majalissar dokokin kasar ta Niger kai tsaye adangane
da maganar zargin cinikin jarirrai, hukumarsa ta rubuta wa Ministan
maaikatar shari'a ta kasa wasika inda ta nemi ya bukaci gwamnati da ta
rubuta wa kwamitin gudanarwa na majalissar dokokin wasika domin neman ya bada iznin a saurari shugaban majalissar dokokin kasar kamar yadda
kuduri mai lamba 88 na kundin tsarin milki da kuma kudiri mai lamba 9
na kundin tsarin aikin dan majalissa su ka tanada.

Alkalin gwamnatin ya ce bayan da kwamitin majalissar ya bada amincewa tuni ya mika takardun soma sauraran Hama Amadou a gaban alkali mai bincike, sai dai kuma sun samu labarin Hama Amadoun ya fice daga kasar, abin da zai biyo baya daga yanzu shine suna jiran sakamakon karar da Hama Amadoun ya shigar a gaban kotun tsarin milki yana mai kalubalantar hanyar da aka bi wajan bada izinin mika shi a hannu kuliya domin daukar matakai na gaba.


"Idan kotun tsarin milki ta tabbatar da halaccin matakin da kwamitin gudanarwar majalissar dokoki ya dauka akan Hama Amadou ,to daga nan babban alkali mai bincike zai bukaci Hama Amadou ya bayyana da kansa a gabansa, idan bai yi haka ba to za a bada izinin a je a taho da shi, daga nan kuma idan aka je ba'a samu ganinsa ba ganin irin yadda ya tsere daga kasar to daga nan alkalin zai rubuta takardar sammacin neman kamo Hamma Amadoun a duk inda ya ke wacce za a rarraba a ko ina ta hanyar hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa ta (Interpol)"


Ya kara da cewa koma ta halin kaka doka ba za ta kasa yin aikinta ba, domin da
zarar alkali mai bincike ya kare bincikensa za'a shigar da takardun a gaban alkali mai shari'a wanda zai yi wa wadanda kenan dama wadanda ba sanan sharia, ya kuma yanke masu hukunci kuma duk ranar da su ka shiga hannu za su biya shekarun kason da za'a yanke masu.

Yanzu dai 'yan Niger sun kashe kunne suna sauraran sakamakon kotun tsarin milkin, kan bukatar karar da Hama ya shigar a gaban ta wanda shine zai nuna alkiblar da rikicin zai dosa nan gaba.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Yusuf Bala

Sauti da bidiyo akan labarin