Za a sulhunta rikicin Yemen | Labarai | DW | 15.03.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a sulhunta rikicin Yemen

Kasashen Larabawa na yankin Gulf na shirin karbar bakwancin tattaunawa da bangarorin da ke rikici da juna a kasar Yemen, ciki har da 'yan tawayen Huthi masu samun goyon bayan Iran, a birnin Riyadh a karshen wannan wata.

Daya daga cikin jami'an kungiyar kasashe shida da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce kwamitin hadin gwiwar kasashen yankin Gulf mai hedikwata a Saudiyya, na tunanin yin shawarwari tsakanin bangarorin da ke rikici da juna a Yemen, don kawo karshen tsamin dangantaka na tsawon shekara da shekaru da ke haifar da zubar da jini.

Wani jami'in gwamnatin Yemen da Saudiyya ke marawa baya, wanda ke fama da rikicin shekaru bakwai da 'yan Huthi, ya ce taron zai gudana ne tsakanin ranar 29 ga Maris zuwa 7 ga Afrilu na shekarar 2022. Sai dai ya kara da cewa da wuya 'yan Huthi su amince da gayyatar da aka yi musu zuwa birnin Riyadh, wadda ke jagorantar kawancen soji don mara wa gwamnati baya kan 'yan tawaye tun shekara ta 2015.

Kusan kashi 80 cikin 100 na al'ummar Yemen kusan miliyan 30, suna dogaro ne da wani nau'i na taimako don gudanar da rayuwar yau da kullum. A  baya-bayan nan hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadin cewa adadin mutanen da ke fama da yunwa a kasar zai karu a bana zuwa 161,000.

Kokarin kira ga bangarorin da ke rikici da juna a kasar Yemen a birnin Riyadh na zuwa ne a daidai lokacin da ake gudanar da wani babban taro na samar da agaji ga kasar Yemen, yayin da ake fargabar cewa mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine na barazana ga samar da abinci a duniya.

Yemen ta dogara kusan kacokan kan shigo da abinci daga kasashen waje, inda kusan kashi uku na kayan alkama ke zuwa daga Ukraine, in ji MDD. Majalisar Dinkin Duniya ta sha yin gargadin cewa kungiyoyin agaji na cigaba da fuskantar karancin kudaden gudanar da ayyuka, lamarin da ya tilasta musu dakile shirye-shiryen ceto rayuwar mutanen da ke cikin bala'in yunwa msuamman a kasashen da ke fama da yaki. A bara Majalisar Dinkin Duniya ta nemi taimakon dala biliyan 3.85, amma ta tara dala biliyan daya da dubu 700 kacal.