Za a fara shari′ar ′yan Boko Haram a Najeriya | Labarai | DW | 09.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a fara shari'ar 'yan Boko Haram a Najeriya

A wannan Litinin za a gurfanar da sama da mutane 1600 da ake zargi 'yan Boko Haram a gaban shari'a, sai dai masu fashin baki a kan al'amuran shari'a na kalubalantar matakin gudanar da shari'ar cikin sirri.

An dai bayyana gabatar da mutanen ne ba tare da inda jama'a suka sani ba, kazalika an yi niyar haramta wa 'yan jaridu da kungiyoyi halartar zaman shari'ar da za a fara a wannan Litinin.

Wadanda ake zargi da ayyukan ta'addancin da za a gabatar da su gaban kuliya, suna a tsare sama da shekaru takwas tun bayan bullar kungiyar Boko Haram. A yanzu ana zargin mutanen da haddasa asarar rayuka akalla fararen hula da jami'an gwamnati sama da dubu 20 a yakunan Arewa maso Gabashin Najeriya.

Wata kididdigar hukuma ta nuna cewa gabannin shari'ar da za a fara a wannan Litinin, mutane tara ne kadai aka yankewa hukunci a cikin mutane 13 da suka fuskanci shari'a a kan zarginsu da ayyukan kungiyar ta Boko Haram.