1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gaza cimma matsaya tsakanin Eu da Birtaniya

December 7, 2020

Tattaunawar da ake dangane da kammala batun ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai na fuskantar nakasu, tattaunawar da zancen kasuwanci tsakanin bagarorin ya mamaye.

https://p.dw.com/p/3mJCp
Boris Johnson und Ursula von der Leyen
Hoto: Peter Summers/Getty Images

Bayan shafe daren jiya ana tattaunawa tsakanin wakillan kungiyar tarayar Turai da na Birtaniya kan makomar kasuwancin bangarorin biyu gabanin ficewar Birtaniyar daga kungiyar ta EU, an gaza cimma matsaya a tattaunawar. Machel Barnier na kungiyar EU da takwaransa daga bangaren Birtaniya David Frost sune suka tattauna a Birnin Brussels na kasar Beljiyam kan yarjejeniyar kasuwanci tsakanin bangarori guda biyu, wadda za a cigaba da ita nan gaba.

Yarjejeniyar kasuwancin dai za ta maida hankali ne kan haraji da kuma shige da ficen kaya tsakanin Birtaniyar da kasashe mambobin kungiyar Tarayar Turai.

Nan gaba kadan ne a ranar Litinin din nan shugaba Boris Johnson na Birtaniya da shugabar kungiyar ta EU  Ursula von der Leyen za su tattauna ta wayar tarho kan batun, gabanin babban taron EU a ranar Alhamis.