1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Za a ci gaba da kai kayan agaji a Gaza

October 23, 2023

Yayin da dakarun Isra'ila suka killace zirin Gaza a wani mataki na murkushe kungiyar Hamas, Amurka da Isra'ila sun yi alkawari za a ci gaba da kai kayan agaji Gaza inda al'amuran jinkai ke dada dagulewa.

https://p.dw.com/p/4XtBM
Motoci dauke da kayan agaji na wucewa ta kan iyakar Gaza da Rafah
Motoci dauke da kayan agaji na wucewa ta kan iyakar Gaza da Rafah Hoto: Mohammed Asad/AP Photo/picture alliance

A daya hannu kuma Amurkar ta gargadi Iran kan yunkurin da ta ke na neman fadada rikicin da ya barke bayan wani munmunan farmakin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra'ila.

Karin bayani:Kayan agaji sun sake isa Zirin Gaza

Wannan gargadi na Washington na zuwa ne bayan da Iran da ke da alaka da kungiyoyin Hamas da Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi hannunka mai sanda ga Amurka da kuma Isra'ila kan yadda suka rufe idanuwa ana cin zarafin bil Adama da kisan kare dangi ba tare da samar da hanyoyin kawo karshen rikicin ba.

Karin bayani:Neman mafita a rikicin Isra'ila da Hamas 

Tuni dai kan wannan furici na Iran, shugaba Joe Biden ya tattauna da hukumomin kasashen Kanada da Jamus da Italiya da Burtaniya da shugaba Emmanuel Macron na Faransa wanda ke shirin kai ziyara Isra'ila. Masu aiko da rahotanni daga yankin sun ce rikicin ya fadada a iyakar Isara'ila da Lebanon da kuma gabar Yamma da Kogin Jordan inda aka ruwaito kisan Palasdinawa 400 a sabon luguden wutar da Isra'ila ta yi a cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza.