Yunkurin karshe na kwato Tikrit a Iraki | Labarai | DW | 14.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin karshe na kwato Tikrit a Iraki

Sojin sa kai na Iraki na cigaba da kokarin da suke yi wajen karbe iko da garin nan Tikrit da ke cikin jerin garuruwan da 'yan kungiyar nan ta IS suka karbe.

Masu aiko da rahotanni suka ce sojin masu yawan gaske ne ke kokarin ganin Tikrit din ta koma karkashin ikon gwamnatin kasar.

Karim al-Nur da ke zaman guda daga cikin masu wannan fafutuka ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar nan da kwanaki uku da ke tafe suke sa ran maida Tikrit din karkashin ikon hukumomin Iraki din.

Sojin na sa kai dai yanzu haka sun yi wa garin kawanya batun da ya sanya mayakan IS din da ba su wuce 70 suka gagara ficewa daga cikinsa.