1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin ceto bankin Credit Suisse a Switzerland

March 16, 2023

Hukumomin Switzerland za su yi taro na musanman domin yin nazari kan makomar bankin ba da rance na kasar wato Credit Suisse wanda hannun jarinsa ya karye.

https://p.dw.com/p/4OmIs
Credit Suisse CEO Ulrich Körner
Hoto: Michael Buholzer/KEYSTONE/picture alliance

Durkushewar bankin da ba a taba samun makamanciyarta ba a Switzerland ta haifar da shakku a fadin kasar tare da saka abokan huldar bankin na Creditn Suisse cikin damuwa.

Tuni dai gwamnatin Switzerland ta umurci babban bankin kasar ta ya ya ranta zunzutun kudi biliyan 50 na kudin kasar wa bankin na Credit Suisse don kubutar da shi daga wannan matsalar tare kuma da kiran masu hannun jari da su ci gaba da mu'amala da bankin.

Gwamnatin Switzerland ta sanar da mahinmancin daukar matakan gaggawa don ceto bankin wanda ke zama na biyu mafi girma a kasar