Yunƙurin warware rikicin gabashin Ukraine | Labarai | DW | 27.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunƙurin warware rikicin gabashin Ukraine

Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Ukraine Petro Poroschenko .

Shugabannin biyu sun tattauna rikicin da ake fama da shi a yankin kudu maso gabashi na Ukraine.

Wanda har kawo yanzu an gaza samun bakin zaren rikicin, duk kuwa da matsin lamba da ƙasashen Ƙungiyar tarrayar Turai ke yi wa Rasha.Wannan tattaunawa na zuwa ne a dai dai lokacin da Ƙungiyar tsaro ta NATO ta zargi Rasha da cewar tana shirin jibge sojojinta a yankin Kirimiya a wani sabon yunƙuri.