1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan waɗanda suka rasu a rushewar wata gada a China ya kai mutum 28

August 14, 2007
https://p.dw.com/p/BuE9

Akalla mutane 28 sun rigamu gidan gaskiya yayin sama da 20 suka jikata lokacin da wata gada ta rushe a kudancin kasar China. Rahotanni na nuni da cewa mutane da dama sun bace saboda haka yawan wadanda suka mutu ka iya karuwa. Gadar wadda ake cikin aikin gina ta ta rushe ne a yankin Fenghuang dake zaman wata cibiyar ´yan yawon shakata a kasar ta China. Kamfanin dillancin labarun hukuma Xinhua ta ce har yanzu ba´a san musabbabin aukuwar hadarin ba amma jami´ai sun fara gudanar da bincike.