1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanciNajeriya

Najeriya: Yaushe za a samu tsaro a Borno?

April 15, 2026

An shiga rudani da damuwa a Monguno da ke jihar Borno, bayan zargin wasu sojoji da kona tare da rushe gidajen talakawa sakamakon kashe kwamandansu a wani hari da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai.

https://p.dw.com/p/5CEfX
Najeriya | Borno | Monguno | Ta'addanci | Boko Haram | Hari | Sojoji | Fararen Hula | Fansa
An jima ana halaka sojojin Najeriya, yayin yakin da suke da ta'addanciHoto: Audu Marte/AFP/Getty Images

A wani mataki da ake ganin na martani kan asarar manyan jami'ansu ne, runudnar sojojin Najeriya ta dauki wannan mataki saboda zargin da suka yi ga wasu mazauna unguwar Chali 2 da rashin bayar da bayanai kan motsin 'yan ta'adda da ma zargin hada kai da su da ma boye su. Sojojin sun fara kona da rushe wasu sassan unguwar, suna mai cewa hakan na da alaka da matsalolin tsaro da kuma zargin cewa yankin na zama hanya da 'yan ta'adda ke bi wajen gudanar da ayyukansu.

Sojoji sun fusata?

Shin an samu karuwar hare-haren 'yan ta'adda a Najeriya?

Daga bisani, an dakatar da aikin na wani lokaci bayan shiga tsakani daga manyan shugabannin sojoji, inda aka tsara yin tattaunawa da shugaban karamar hukumar Monguno da shugabannin al'umma. Sai dai mazauna yankin sun ce sojojin sun sake komawa suna kona gidaje, lamarin da ya kara tayar da hankula kan yiwuwar gazawar kokarin sasanta rikicin. Wannan lamarin ya jefa al'umma cikin fargaba, inda wasu mazauna suka rika tserewa domin tsira da rayukansu yayin da ake zargin an lalata gidaje da dukiyoyi.

Karuwar rashin yadda

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi tir da wannan mataki da ake zargin sojojin da dauka, wanda suka ce hakan zai bata dangantaka tsakanin al'umma da jami'an tsaro. Wannan ma kuma shi ne fahimtar masana da masharhanta kamar Malam Abubakar M Kareto da suka ce, idan dangantakar ta baci abin zai iya shafar ayyukan jami'an tsaro da yaki da ta'addanci. Har ya zuwa yanzu hukumomin soja ba su fitar da cikakken bayani kan zargin ba, yayin da ake ci gaba da jiran karin haske kan abin da ya faru kuma duk kokarin ji daga bangarensu ya ci tura.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani