Yarjejeniyar kasuwancin bai daya a Afirka | Siyasa | DW | 09.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yarjejeniyar kasuwancin bai daya a Afirka

Kungiyar Tarayyar Afirka ta cimma yarjejeniyar kasuwancin bai daya, batun da kafin yanzu ake ganinsa a matsayin wani mafarki. Fatan 'yan kasuwar nahiyar dai shi ne, ganin cewar an tabbatar da aiwatar da ita

Wannan dai wani yunkuri ne na karfafa tattalin arzikin nahiyar Afirka, kuma a yanzu dunkulalliyar kungiyar kasuwanci ta kasashen Afirka mai wakilai54, za ta kasance mafi girma cikin kungiyar kasuwanci ta duniya wato WTO.

Bisa waiwayen bala'in fadawa cikin teku da 'yan gudun hijirar Afirka ke yi a kullum, hakan ya sa kowa na yiwa Afirka fatan samun farfado da tattalin arzikin nahiyar cikin gaggawa. To sai dai kusan akasarin irin wadannan yarjejeniyoyin da Afirka kan cimma a takarda kawai yake tsayawa, domin tun a shekarata 1980 Kungiyar kasashen Afirka da lokacin ake kira OAU ta cimma kudurin kasuwanci tsakanin wakilanta. Wancan lokacin a  kudurin da suka cimma a birnin Lagos na Najeriya, bawai ga kasuwancin bai daya aka amince ba, amma har da batun samar da takardun kudi na bai daya ta kasashen Afirka.

Haka kuma an amince cewar a manyan biranen kasashen 54 a gina musu layin dogo na jiragen kasa masu saurin tafiya na zamani.  Sai dai babbar matsalar akasari babu wutar lantarki babu kuma tituna masu kyau, kana ga matsalar sadarwa.

A kan iyakokin kasashen Afirka tireloli na yin kwana da kwanaki suna yin layi su na tsaye bisa jiran izinin wucewa. A bangaren jiragen sama, mutun daga Afirka yazo nahiyar Turai na da matukar sauki fiye da in ya ce zai tafi daga wata kasar Afirka izuwa Afirka. Kasashen Afirka basu yarda da juna ba, hakan na nuna baza su rika yin la'akari da pFasfon bai daya na Afirka ba.

Kawo yanzu babu kasuwanci bai daya na Afirka

Kason kasashen Afirka a bangaren kasuwancin duniya, tun shekaru 20 bai sauya ba, inda nahiyar ke samar da kaso biyu da rabi cikin dari. Hakan na nufin gabadayan kasuwancin Afirka bai kai na kasar Japan kadai ba.

Bunkasar tattalin arzikin nahiyar ya samu koma baya da kashi uku cikin 100 a kwanakkinnan, musamman hajojin da Afirka ta dogara da su wajen kasuwanci da kasashen waje, wato zinari da mai da lu'l'u da karafa da Koko. A yanzu kasuwanci tsakanin kasashen Afirka su ya su yana samar da kashi 12 cikin 100.

A Nahiyar Afirka ana da hajojin kasuwancin da za su iya gogayya da ko wace nahiya ta duniya. To sai dai a cewar hukumar tattalin arzikin Kungiyar Tarayyar Afirka, sufurin kaya tsakanin Afirka yafi na ko wace nahiya tsada a duniya. Misali idan an dauko kontena daya daga Tokyo kasar Japan, mutun zai biya kimanin euro 1.300 a kai masa ita Abidjan, kasar Cote' d'voire, yayin da in ka dauko kontena daya daga Addis-Ababa kasar Habasha sai ka biya Euro 4.500 kafin a kai maka ita Abidjan, kasar Cote' d'voire. Wato dai sama da rubi uku.

Wannan ya sa za ka ga misali mutun ya sayi tsohuwar mota daga Japan ya kawo Zimbabuwe, maimakon ya tsaya sayen wata sabuwar VW ko Nissan ko BMW da aka kera a nahiyar Afirka. Shugabannin Afirka dai na ta yin murnar kulla yarjejeniya a Yamai. Walau ko za ta zama yarjejniyar tarihi, za dai mu gani, domin da farko abun jira shi ne ko siyasarsu za ta tabbatar da kasuwancin da suka cimma tsakaninsu.

 

Sauti da bidiyo akan labarin