Yarjejeniyar izinin yawo tsakanin kasashen turai | Zamantakewa | DW | 20.12.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yarjejeniyar izinin yawo tsakanin kasashen turai

A gobe ne yawan kasashen yarjejeniyar Schengen zai kai 24

default

Schengen

Bayan shekaru goma da gabatar da yarjejeniyar Schengen dake kawar da bincike tsakanin kasashen Turai, tun daga yau juma’a za a samu ƙarin ƙasashe a yarjejeniyar wanda zai kai adadinsu zuwa .kasashe 24. Maziyarta masu yawon bude ido daga ƙasashen Amurka da Japan su kan shiga mamakin ganin yadda suke da ikon ratsa ƙasashe daban-daban na Turai ba tare da an binciki takardunsu na fasfo ba. Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da suka sanya shugaban hukumar zartaswa ta Ƙungiyar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya ɗokata wajen bayyana murnarsa da ci gaban da aka samu na karin ƙasashe a ƙarƙashin yarjejeniyar Schengen. Barroso ya ce:

“Tun dai abin da ya kama daga 21 ga watan disimba mutane zasu samu ikon kai da komo tsakanin ƙasashe 24 ba tare da wata tsangwama ba. Wannan wani muhimmin ci gaba ne na tarihi. Kawar da iyakokin zai bai wa jama’a wata sabuwar dama ta zirga-zirga da ƙulla hulɗoɗi na kasuwanci. A saboda haka a ganina wannan wannan wani babban ci gaba ne akan hanyar tabbatar da haɗin kan nahiyar Turai.”

To sai dai kuma mahukunta na ‘yan sandan tsaffin ƙasashen dake da hannu a yarjejeniyar ta Schengen sun bayyana fargabarsu a game da fuskantar karuwar sace-sacen motoci da miyagun laifuka da kuma tuttudowar baƙin haure. A ganinsu karuwar yawan ƙasashen yarjejeniyar abu ne da zai ƙara haifar da ruɗami da rashin sanin tabbas. Amma kakakin hukumar zartaswa ta Ƙungiyar Tarayyar Turai akan manufofin shari’a da tsaro ya ƙalubalanci wannan iƙirari yana mai cewar:

“Babu wani mahaluƙin da zai iya tabbatar da tsaron iyaka ɗari-bisaɗari. An fuskanci wannan matsalar kafin a gabatar da yarjejeniyar Schengen. A saboda haka muke bakinƙoƙarinmu wajen kare iyakokin ƙasashen dake da iyaka da ƙasashen da ba na Ƙungiyar Tarayyar Turai ba tare da ƙwararrun ma’aikata da na’urori na zamani.”

A yanzun dai wadannan iyakokin na ƙasashen Schengen zasu fi shafar iyaka ne tsakanin Poland da Bailorushiya, sannan a lokaci guda kuma za a ƙara kyautata hadin kai tsakanin ƙasashen da lamarin ya shafa. Kawo yanzu mahukuntan na amfani ne da komputa domin musayar rahotanni tsakaninsu ko da yake ƙwararrun masana sun nuna cewar tsarin da ake amfani da shi tuni ya zama tsofon yayi. Amma duk da haka Frisco Roscam Abbing ya ce ba zata yiwu a dakatar da karɓar ƙarin ƙasashe a yarjejeniyar ta Schengen har sai an sabunta tsare-tsaren na’urar ta koputa ba, saboda dukkan binciken da aka gudanar ya nuna cewar sabbin ƙasashen sun cika sharuɗɗan da ake bukata. Kakakin hukumar zartaswar ta Ƙungiyar Tarayyar Turai ya ƙara da cewa:

“Ba lalle ba ne ba a jira har sai shekara ta 2008 lokacin da za a kammala sabbin tsare-tsaren, saboda tuni aka cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa. Bugu da ƙari kuma an tabbatar da tsaron iyakokin ƙasashen dake da iyaka da ƙasashen da ba na Ƙungiyar Tarayyar Turai ba.”

 • Kwanan wata 20.12.2007
 • Mawallafi Ahmad Tijani Lawal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/CeAL
 • Kwanan wata 20.12.2007
 • Mawallafi Ahmad Tijani Lawal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/CeAL