Yarjejeniyar amincewa da sakamakon zabe a Najeriya | Labarai | DW | 26.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar amincewa da sakamakon zabe a Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan da Janar Muhammadu Buhari sun amince da sabuwar yarjejeniyar yin zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Kimanin kwanaki biyu da a gudanar da zaben shugaban kasa a tarayyar Najeriya manyan jam'iyyun kasar biyu wato PDP da APC da kuma 'yan takarar da ke musu jagora sun dauki alkawarin mutunta sakamakon zaben komai daci. A wani taron da ya samu halartar manyan 'yan kwamitin tabbatar da sake zaman lafiya da safiyar wannan Alhamis a Abuja, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da kuma jagoran 'yan adawa Janar Muhammadu Buhari sun rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar tabbatar da zaben a cikin masalaha sannan kuma da amincewa da sakamakon da zai fito a cikinsa. A ranar Asabar za a gudanar da zaben da ake fargabar samun tashin hankali a cikinsa.