Yara masu cutar Aids na samun Kulawa | Himma dai Matasa | DW | 08.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Yara masu cutar Aids na samun Kulawa

A karan farko a Najeriya an sami wata mace mai fama da ciwon HIV/AIDS ko Sida a Kaduna, da ke renon kananan yara marayu masu cutar kanjamau tare da ba su horo kan sana’o’in hannu da ba su ilimi.

Malama Aisha Usman ta kasance daya daga cikin shugabannin kungiyoyin mata masu fama da cutar HIV/Aids ko Sida a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya, ta koma tattaro kananan yara marayu da ke fama da cutar wadan da iyayen su suka rasu sanadiyyar kamuwa da cutar da nufin karesu daga fuskantar tsangwama da kyama a cikin alumma.

A yanzu dai Aisha na ci gaba da ba wa irin wadannan yara kyakkyawar kula tare da ba su horo na musamman kan sanao'in hannu, tana kuma sa su a makarantun Boko da na Allo domin samun ilimin addini da na zamani ta yadda za su yi dogaro da kansu anan gaba.