1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin sakin daya daga cikin 'yan matan Dapchi

August 23, 2018

Iyayen Leah Sharibu, daya daga cikin daliban makarantar Sakandire ta Dapchi da ke hannun mayakan Boko Haram sun yi kira ga gwamnati da ta yi wani abu dan ganin 'yarsu ta dawo ga hannunsu.

https://p.dw.com/p/33dDu
Makatantar Sakandiren Dapchi a Najeriya
Makatantar Sakandiren Dapchi a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/A. Abubakar

A watan Febrairu ne dai na wannan shekarar ta 2018 mayakan Boko Haram suka sace daliban makarantar sakandiren Dapchi a jihar Yobe, inda suka sako su a watan Maris ba tare da Leah Sharibu ba, wadda ta ki amnicewa ta shiga addinin musulunci kamar yadda wadanda suka sace ta suka nema kafin su sako ta, abinda ya sa suka dawo da sauran ita kuma suka ci gaba da rike ta a hannun su. Sharibu Nathan mahaifin Leah ya bayyana halin da suke ciki tun bayan sace 'yar tasu inda ya ce hali ne na takaici da fatn ganinta a kullu yaumin.

Wasu daga cikin 'yan matan sakandiren dapchi da aka sallamo
Wasu daga cikin 'yan matan sakandiren dapchi da aka sallamoHoto: DW/A.S. Muhammad

Ita ma malama Rabecca Sharibu mahaifiyar Leah, roko ta yi ga gwamnatin Tarayyar Najeriya da sauran jami'an tsaro su yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin an ceto mata ‘yarta kamar yadda aka ceto sauran wadanda aka sace su tare. Iyayen dai sun ce duk da su na cikin mawuyacin hali saboda rashin dawowar ‘yar su tsawon lokaci irin addu'o'i da Musulmi da kirista ke yi na kwantar musu da hankali gami da basu kwarin giwar ‘yar su za ta dawo gare su wata rana.

Karikatur: Dapchi Mädchen
Hoto: DW

Rev Daniel Auta, shi ne shugaban Cocin da Leah ke halarta ya bayyana ta a matsayin mai hankali da biyayya ga kowa da kowa. Kawayen Leah da wadan su ke makaranta daya sun ce su na kewarta matuka inda suke rokon hukumomi su kara kaimi wajen ganin an dawo da ita. Baban abinda iyayen suka yi kuka da shi a wannan lokaci shi ne rashin samun wani bayani daga gwamnati ko jami'an tsaro kan irin kokarin da ake yi na ceto ‘yar ta su.  Sai dai a baya shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin ceto Leah da ma sauran daliban makarantar sakandaren Chibok da suka kwashe shekaru a hannun mayakan na Boko Haram.