Yankunan da aka kwato daga Boko Haram | Siyasa | DW | 07.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yankunan da aka kwato daga Boko Haram

Tawagar 'yan jaridun Tarayyar Najeriya ta kai ziyarar gani da ido garuruwan Bama da Konduga na jihar Borno, da sojojin kasar suka kwato daga hannun kungiyar Boko Haram.

Halin kuncin rayuwa a Bama

Halin kuncin rayuwa a Bama

Da zarar ka shiga ka shiga farfajiyar Kanawuri a kan hanyar zuwa Bama, ba abin da zaka ji sai karar jiragen yaki abinda ke sanar da kai cewa a fagen yaki kake. Tafiya ce dai ta kilomita 70 daga Maiduguri zuwa Bama, amma an yi kaca-kaca da daukacin matsagunan da ke kan hanyar zuwa Baman. 'Yan jaridar dai sun iske birnin Bama da aka kiyasta ya kunshi mutane dubu 250 ya koma tamkar kufai, domin in banda sojoji da ‘yan kato da gora ba bu wani mahalukin da ke kwana a birnin kowa ya arce. To shin wane hali ake ciki a garin Bama ne a yanzu? Major General Yusha'u Muhammad Abubakar shine kwamnadan rundunar sojoji da ke yaki a yankin Arewa maso Gabas na Najeriyar ya kuma shaidawa wakilinmu Uwais Abubakar Idris da ke cikin ayayrin 'yan jaridar cewa:

Boko Haram ta yi ta'adi mai yawa

Boko Haram ta yi ta'adi mai yawa

Garuruwa sun zama kufai

"Kasan in ka dubi tarihin abin da ya faru a Bama nan ne shelkwatar ‘yan Boko Haram mun zaga da kai ka ga irin barnar da suka yi, amma a kullum muna samun nasara."

Ganin irin yadda aka yi kaca- kaca da garurwan Bama da Kwanduga da kuma Kanawuri ya sanya tambayar ministan yada labarai da al'adun gargajiya na Najeriya Lai Mohammed wanda ke cikin tawagar ko me yafi daga mashi hankali?

Ya ce: "Abin da yafi girgiza ni shi ne irin mummunar barnar da aka yi a nan. Mafi yawanmu kafin mu zo nan ba mu san irin barnar da yaki ya haifar ba, bama wannan ne abin damuwa ba sai irin mummunan halin da aka jefa mata da yara kanana a ciki. Ina fatan wannan zai zama darasi a gare mu baki daya."

Mutane da dama na gudun hijira

Mutane da dama na gudun hijira

Akwai dai dubban marayu mata da yara kanana, wanda babu tambaya kasan suna cikin tashin hankali, abin da yafi daga hankali shi ne lokacin da aka tambayi wani yaro ina babanka yace yana Maiduguri, bai san cewa an kashe mahaifin nasa ba. Duk da kokarin hana magana da wasu 'yan gudun hijirar da sojoji suka yi dai 'yan jaridun sun gana da wasu.

Yunkurin gyara garuruwan da aka lalata

Ga kwamshinan yada labarai na jihar Borno Bulama Muhammad ya ce abin da ke gabansu shi ne kokarin sake gina wuraren da aka lalata, domin baiwa mutane ikon komawa gidajensu, amma abin tambaya shi ne har zuwa wane lokaci zasu yi hakan? Sojojin da ke wannan aiki dai sun nuna annashuwa da samun kwarin gwiwa da ziyarar da aka kai da ma jawabin da ministan yada labarai ya yi musu. Ga dukkanin wanda idanunsa basu gane masa ba sai dai a kwatanta masa irin barnar da aka yi, domin babu kalmomin da za su iya yin cikakken bayani na mummunan halin da ake ciki a wannan yanki.

Sauti da bidiyo akan labarin