1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: 'Yan M23 za su ajiye makamai

March 7, 2023

Kungiyar 'yan tawayen M23 na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta ce, ta kudiri aniyar mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta wacce ke fara aiki Talatar wannan mako.

https://p.dw.com/p/4OMwL
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango I 'Yan tawaye | M23
'Yan tawayen M23 da suka addabi gabashin Kwango za su ajiye makamaiHoto: Guerchom Ndebo/AFP

Wannan mataki dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke kokarin isar da kayan agaji ga dubban al'umma a gabashin Kwangon, wadanda yakin ya ritsa da su. Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar za ta kai tallafi zuwa birnin Goma tare da hadin gwiwar Faransa, domin kai dauki ga mazauna wannan birni da ke gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon da kusan 'yan tawayen M23 suka yi musu zobe. Kungiyar ta EU ta ce za ta bayar da kudi Euro miliyan 47 ta hanyar abokan huldarta na jin kai, domin biyan bukatun al'ummar yankin musamman na abinci da kula da lafiya da tsaftar muhalli. Kungiyoyin farar hula sun yi marhabin da wannan labari mai dadin ji, in ji Marrion Kambale shugaban hadin gwiwar kungiyar farar hula da ke birnin na Goma.

Kwango I Rundunar wanzar da zaman lafiya ta kasashen gabashin Afirka | M23
Rundunar wanzar da zaman lafiya ta kasashen gabashin Afirka da 'yan tawayen M23Hoto: Guerchom Ndebo/AFP

Sai dai ya ce mutanen da ke cikin mawuyacin hali suna bukatar ruwa ko magunguna, amma sama da komai suna bukatar su koma su zauna lafiya a kauyensu na asali maimakon zama a sansanonin 'yan gudun hijira. Mutanen sun fice daga garuruwansu da ke arewacin Kivu saboda 'yan tawayen sun yi sansani a wurin, to amma kungiyar ta M23 ta ce daga ranar Talata bakwai ga watan Maris za ta daina kai hare-hare domin muntata yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsu da gwamnatin. Augustin Muhesi masanin kimiyyar siyasa a Goma ya ce, ba za a yi gaggawar aminta da furcin 'yan tawayen ba har sai sun aiwatar da alkawarin nasu. A wani yunkuri na dakile ci gaban 'yan tawayen M23 da kuma korar kungiyoyin da ke dauke da makamai a yankin gabashin Kwango wadanda suka zarta 100, an tura sojoji a matsayin wani bangare na rundunar kasashen yankin Tsakiyar Afirka domin tabbatar da tsaro wato EAC.