1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawaye sun mutu a hare-hare a Yemen

Mouhamadou Awal Balarabe
October 12, 2021

kawancen sojojin da Saudiyya ke jagoranta a Yemen ya yi ikirarin kashe 'yan tawayen Huthi 300 a cikin sa'o'i 48 da suka gabata, a cikin samamen da sojojin gwamnatin kasar suka kai a yakin Marib da ke arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/41b3R
Jemen | Kämpfe in Marib
Hoto: AFPTV/AFP/Getty Images

Gidan talabijin na al-Ekhbariya na Saudiyya ya ruwaito cewa sama da 'yan tawayen Huthi 134 sun halaka a hare-haren da aka kai a Al-Abdiya", yayin da a ranar Litinin, kawancen ya ba da sanarwar mutuwar 'yan Huthi 156" a farmakin da aka kai a wannan yanki na Marib. Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari.

Daruruwan mayaka sun halaka tun watan Fabrairu a yakin Marib, inda 'yan tawayen suka tsananta kai hare -hare a cikin watannin da suka gabata, kuma suka zarce zuwa babban birnin kasar ta Yemen. Ba safai ne 'yan Huthi suke sanar da adadin wadanda suka mutu a sansaninsu ba.

Yemen ta kasance fagen yaki tun shekarar 2014 tsakanin dakarun da ke goyon bayan gwamnati da 'yan tawayen Huthi da ke iko da yawancin arewacin kasar ciki har da Sana'a babban birni.  A cikin wadannan shekaru bakwai na yaki, an kashe dubun dubatan mutane, akasarinsu fararen hula, kuma miliyoyin sun rasa muhallansu, a cewar kungiyoyin kasa da kasa.