1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

An cafke mai kurarin tayar da abin fashewa a Paris

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 19, 2024

Jami'an jakadancin Iran ne suka ankarar da 'yan sanda abin da ke faruwa, bayan ganin mutumin sanye da jigidar daura abubuwa masu fashewa a jikinsa

https://p.dw.com/p/4ezl0
Hoto: Benoit Tessier/REUTERS

Rundunar 'yan sandan Faransa ta samu nasarar cafke mutumin nan da ya yi kurarin tayar da abin fashewa a jikinsa bayan kutsawa cikin ofishin jakadancin Iran a birnin Paris.

Karin bayani:Iran ta yi allawadai da hare-haren da Amurka da Burtaniya suka kai Yemen

Bayan kama shin ne suka bincike shi tare da motarsa, amma ba su samu komai na fashewa a tare da shi ba, kuma za su gurfanar da shi gaban kotu a ranar Litinin mai zuwa.

Karin bayani:An tsaurara tsaro bayan dan sanda ya aikata kisa a Faransa

Ko a cikin watan Satumban bara ma an taba kama shi da yunkurin kunna wuta a ofishin jakadancin Iran din na Paris.

Jami'an jakadancin Iran din ne dai suka ankarar da 'yan sanda abin da ke faruwa, bayan ganin mutumin sanye da jigidar daura abubuwa masu fashewa a jikinsa.