′Yan sanda sun kama masu bore 300 a Rasha | Labarai | DW | 03.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda sun kama masu bore 300 a Rasha

‘Yan sandan Rasha sun kama sanannen dan adawan kasar Lyobov Sobol bayan da ya kira magoya bayansa su fito gudanar da sabuwar zanga-zanga da ta samu karbuwa a babban birnin kasar wato Moscow.

Sai dai duk da dokar haramta zanga-zangar da 'yan sanda suka kafa, daruruwan mutane sun bazama kan titunan birnin kasar, wasu rahotanni daga birnin Moscow na cewa kusan masu zanga-zangar 300 'yan sanda suka tsare.

Shi dai Sobol yana aiki kafada da kafada da fitaccen mai sukar manufofin gwamnatin Kremlin Alexei Navalny, wanda yanzu haka yake tsare a hannun hukumomin Rasha.