1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaduna: Cafke wadnada suka sace dalibai

Abdul-raheem Hassan
May 19, 2022

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama wasu mutane biyu da take zargi da hannu a sace dalibai 20 a kwalejin Greenfield da ke jihar Kaduna a shekarar 2021.

https://p.dw.com/p/4BZtw
Nigeria Demo gegen Polizeigewalt in Lagos
Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture-alliance

Hukumar 'yan sandan ta kama Aminu Lawal wanda aka fi sani da Kano da kuma Murtala Dawu wanda aka fi sani da Mugala kan zargin su da hannu a harin da aka kai da makamai a makarantar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani jami'in makarantar. Za'a gurfanar da su a gaban kotu idan 'yan sanda sun kammala bincike.

Idan ba a manta ba, 'yan bindigar sun saki mutane 14 cikin mutane 20 da suka yi garkuwa da su bayan kwanaki 40 da sace su, sun kashe mutane biyar don tilastawa iyalai da gwamnati biyan kudin fansa.

Yanzu haka dai akwai akalla 'yan makaranta 1,500 a hannun masu garkuwa da mutane, inda dalibai 16 suka rasa rayukansu a cewar Asusun kula da Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF.