1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Najeriya na martani kan sauyin ranakun zabe

Muhammad Bello
February 27, 2026

'Yan Najeriya da dama na baiyana ra'ayoyi mabambanta kan sauyin ranakun zaben 2027 da hukumar zaben kasar INEC ta sanar wanda ya janyo cece-kuce

https://p.dw.com/p/59YcQ
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a wajen wani taro
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a wajen wani taroHoto: James Oatway/REUTERS

Bemene Tanem dan yankin Ogoni, ya ce babu korafi kan sauya ranar zabuka da hukumar zabe ta kasa INEC ta yi, inda korafin ya ke shi ne dalilan da aka bayar na sauya ranakun zaben ganin ba dadewa da fidda sanarwar ranakun gudanar da zabukan, hakan na sa tantamar ko hukumar ta INEC na zaman kan ta ne ko dai akwai masu juya ta daga bayan fage. Na tabbatar INEC za ta kammala dukkanin shirye-shirye kafin sanarwar farko, yanzu kuma an sauya ranakun wadda ke nuna da walakin goro a miya. Me ta hango da bamu hango ba, menene dalilansu.

Eric Omare lauya ne, kuma ga abin da ya ke cewa.

Jami'in zabe a Najeriya
Jami'in zabe a NajeriyaHoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture alliance

"Ya ce a ganina sauya ranakun zabe bai rasa nasaba da dalilai biyu, na daya korafin da alummar musulmin kasar suka gabatar, na biyu sauye sauyen dokoki da aka samu na shekarar 2026 da mu ke ciki kan zaben, babban abin la'akari da shi a yanzu shi ne cewar duk da sauyin ranakun zabuka, babu wani abun damuwa sosai".

Ya ce ina ganin babu wani laifi hakan da INEC ta yi, domin mataki ne na sauraron al'ummar Kirista da kuma Musulmi, domin dukkaninsu suna zarrufa da ranakun farko suka yi wa kancal. Musulmi musamman suna azumi a lokacin, za su so a saukaka musu, haka kuma muna fatan INEC din za ta yi amfani da naurar hanzarta fidda alakaluman zabe, kuma da fatan za a kare mana sahihancin kuriunmu.

Else Emwanta cewa ta yi.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a wajen wani taro
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a wajen wani taroHoto: Nengi Nelson/REUTERS

"Ta ce akwai kokekoke daga jamaa tun farko, musamman kan yadda ranakun zaben da hukumar zabe ta kasa ta sanar, da suka yi karo da ranakun watan Ramadan da Musulman kasar ke azumtar sa".

A gaba dayan abun dai, bisa la'akkari da Dimukuradiyya ta kwarai, akwai bukatar komai ya zamo a bayyane da cikakken shirin daukacin masu ruwa da tsaki a harkokin zaben da gudanar da aikin wayar da kawunan jama'a da tanadar kayayyakin zabe da uwa uba shiri sosai kan tsaro ta yadda zai dace da sabbin ranakun zaben. Haka kuma dole a tabbatar da gaskiya da adalci a zaben, tare da ganin an bai wa kowa damar zabe da kuma tabbatar da sahihancin alkaluman zaben da INEC za ta fidda.

Achi Opaga shi ma Lauya ne, daga yankin kudu maso gabashin kasar.

Wasu matasa 'yan Najeriya
Wasu matasa 'yan NajeriyaHoto: DW

Ya ce hukumar zabe mai zaman kanta INEC doka ce ta kafa ta, kuma sauyin ranakun bai rasa nasaba da wasu 'yan sauye-sauye da aka samar a dokokin zaben kasar, sauye-sauye na shekarar 2026 ke nan da mu ke ciki, wadda yan majalisun kasar biyu suka yi aiki a kai. Dan haka babu haufi kan wannan, Babban batu dai yanzu shi ne jan kafar da hukumar zaben ke yi kan amfani da naurar IREV mai hanzarta fidda alkaluman zabe, amma kuma bankuna kan iya samar da fasahar hakan, ka tura kudi, ka san balas din kudi duka nan take, sannan kuma Yan bindigar daji na da karfin Internet din da suke aikawa da sakonni nan take, amma ace hukumar INEC ba za ta iya ba, wai babu karfin Internet a kauyukanmu.