′Yan Mujao sun dauki alhakin kisan sojojin Nijar | Siyasa | DW | 06.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan Mujao sun dauki alhakin kisan sojojin Nijar

Daya daga cikin jagororin 'yan Jihadi na kasar Mali, na kusa da kungiyar Mujao, ya dauki alhakin kai harin da yayi sanadiyar rasuwar sojojin Nijar guda tara a arewacin kasar ta Mali

Shi dai wannan dan jihadin dan kasar ta Mali, mai suna Sultan Ould Bady, dake da kusanci da kungiyar Mujao, cikin firar sa da kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP cewa yayi, da sunan dukkan 'yan Mujahiddine, sun kai hari ga dakarun kasar Nijar dake ayuka tare da makiyan adinin Muslunci, inda yace da karfin Allah harin da suka kai ya hallaha dakarun kasar ta Nijar guda tara, inda yace makiya su sani cewa munddin dai basu bar wannan kasa ba, to ba zasu taba samun kwanciyar hankali ba.

Sai dai daga nasu bengare hadin gwiwar kungiyoyin fararan hulla na kasar Jamhuriyar Nijar, da ma hukumomin wannan kasa, sunyi Allah wadai da wannan hari na ta'adanci da yayi sanadiyar mutuwar sojojin kasar tare da yin kira ga al'ummomin yanki da su bada cikeken hadin kai wajan gano muyagun mutanen 'yan ta'adda. Shi dai dama Sultan Ould Bady, a baya ya sha daukan alhakin hare-haren da kungiyoyin su ke aikatawa a arewacin kasar ta Mali da sunan dukkanin kungiyoyin 'yan Jihadin dake wannan yanki.

Kungiyar Mujao mai alaka da kungiyar Al-Qaida na daga cikin kungiyoyin da suka kame arewacin kasar ta Mali a shekarar 2012 zuwa farkon shekarar 2013, kafin dakarun kasa da kasa bisa jagorancin kasar Faransa su kore su, inda ake ganin duk da cewa an rage musu karfi, amma kuma wadannan kungiyoyi na nan da ran su a cikin wadannan yankuna inda suke gudanar da ayuka na sari ka noke dake haddasa rasuwar mutane da dama. A halin yanzu dai, dakarun na Minusma na neman wadannan 'yan ta'adda ruwa a jallo ta yadda zasu gurfana a gaban kuliya.

Sauti da bidiyo akan labarin