1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan matan Najeriya sun taka rawar gani

Lateefa Mustapha Ja'afar MAB
October 24, 2022

A karon farko 'yan matan Najeriya 'yan kasa da shekaru 17 sun kai wasan kusa da na karshe a cin kofin kwallon kafa na duniya. Bochum ta bayar da mamaki, bayan da ta lallasa Union Berlin da ke saman teburin Bundesliga.

https://p.dw.com/p/4IcCA
'Yan matan Super Falcon ta NajeriyaHoto: Simone Scusa/Shengolpixs/IMAGO

Masana da kwararru kan harkokin wasanni a Najeriya sun jinjina wa tawagar kungiyar kwallon kafa ta mata 'yan kasa da shekaru 17 wato flying flamingos, dangane da nasarar da ta samu na kai wa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da yanzu haka ake fafatawa a kasar Indiya. Kungiyar dai ta doke kasar Amirka kafin kai wa ga matakin na kusa da na karshe, wanda hakan ya kasance karon farko da kungiyar ta taba yin irin wannan kokari a tarihinta. 

Formel 1 Großer Preis von Japan Suzuka | Sieger Max Verstappen Red Bull
Lokacin da Max Verstappen ya lashe tseren motoci a Japan Hoto: KIM KYUNG-HOON/REUTERS

Verstappen na fatan sake lashe tseren motoci

Shahararren zakaran tseren motoci na duniyar Max Verstappen na fatan sake lashe kambun tseren motocin a karo na 15, yayin  babbar gasar da za a fafata a jihar Texas ta Amirka. An dai jima ana damawa da Verstappen mai shekaru 25 a duniya da kuma ke zaman ruwa biyu, wato dan kasashen Holland da kuma Beljiyam.       

Shi kuwa shararren dan damben ajin masu nauyi Tyson Fury na shirin fafatawa da Derek Chisora a karo na uku a birnin Tottenham na kasar Ingila. Mai shekaru 34 a duniya, na shirin fafatwa da tsohon dan wasan damben Chisora a ranar uku ga watan Disambar wannan shekara ta 2022 da muke ciki, bayan da ya samu nasara a kan Chisora a shekarun 2011 da kuma 2014. Sai dai har yanzu, babu wani tabbaci kan batun fafatawarsu da Anthony Joshua na Birtaniya da tauraruwarsa ke haskawa a bangaren damben ajin masu nauyin.

Fußball Bundesliga | VfL Bochum - Union Berlin
'Yan wasan Bochum sun bai wa na Union Berlin mamaki a BundesligaHoto: Teresa Kroeger/nordphoto/IMAGO

Laya ta yi wa Bochum kyau rufi a Bundesliga

Kungiyar kwallon kafa ta Union Berlin da ke saman teburin Bundesliga ta kwashi kashinta a hannun Bochum da ci biyu da daya a fafatawar da suka yi a ranar Lahadi. Wannan wasa ya bayar da mamaki, ganin yadda Union Berlin ke ci gaba da rike wuta a saman tebur, yayin da Bochum din ta gaza katabus. Haka ma a bin yake tsakanin Hertha Berlin da Schalke 04, inda suka tashi wasa Hertha Berlin na da ci biyu Schalke na da ci daya.

Borussia Dortmund ta yi ruwan kwallaye da ci biyar da nema a ragar Stuttgart. An kuma tashi wasa canjaras uku da uku tsakanin Augsburg da Leipzig, kana Frankfurt ta bi Borrussia Mönschengladbach har gida ta caskara ta da ci uku da daya. An tashi wasa biyu da biyu tsakanin Bayer Leverkussen da Wolfsburg, yayin da Freiburg ta samu nasara a kan Werder Bremen da ci biyu da nema. Ita ma dai kungiyar Bayern Munich ta bi Hoffenheim har gida, ta kuma ba ta kashi da ci biyu da nema. Ita kuwa Mainz ta zazzaga kwallaye biyar a ragar Cologne, inda aka tashi wasan Mainz na da ci biyar Cologne na nema.

Har yanzu dai Unioin Berlin ce a saman tebur da maki 23, yayin da Bayern Munich ke biye mata da maki 22 sai kuma Freiburg a matsayi na uku da maki 21.

BdTD | UK, Londen - Premier League - Arsenal v Crystal Palace
Arsenal ta saba cin kwallo idan tana karawa da abokan hamayyartaHoto: Hannah Mckay/REUTERS

Har yanzu Arsenal na saman teburi a gasar Ingila

A gasar Premier League ta Ingila kuwa, an tashi kunne doki daya da daya tsakanin Arsenal da Southhapton, kuma bai hana Arsenal ci gaba da zama saman tebur da maki 28 ba. Manchester City ke a matsayi na biyu da maki 26, bayan da ta lallasa Brighton da ci uku da daya. Ita ma dai Tottenham ta ci gaba da rike matsayi na uku da maki 23, duk kuwa da kashin da tasha a gida a hannun Newcastle da ci biyu da daya. A sauran wasannin kuwa, an tashi kunnen doki daya da daya a fafatawa taakanin Chelsea da Manchester United. Liverpool ta sha kashi da ci daya mai ban haushi a gidan Everton, inda Leicester ta bi Wolverhampton har gida ta yi caskara ta da ci hudu da nema.