′Yan jarida na fuskantar muzgunawa a duniya | Labarai | DW | 15.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan jarida na fuskantar muzgunawa a duniya

A shekara 2015 'yan jariodu 54 aka yi garkuwa da su a duniya kana ana tsare da wasu 153 a gidajen kurkuku a cewar Reporters sans frontières.

Irak Pressefreiheit Symbolbild

Wasu 'yan jarida a Iraki

A cikin rahotanta na shekara da ta bayyana Ƙungiyar 'yan jarida ta ƙasa da ƙasa Reporters Sans Frontiere, ta ce a cikin wannan shekara ta 2015 an fi yin garkuwa da 'yan jarida fiye da shekara bara.Yayin da kuma aka samu ragowar sace 'yan jarida, ƙasa kwarai ga shekara da ta shuɗe.

A cikin wannan shekara da take shirin ƙarewa 'yan jaridu 54 aka yi garkuwa da su a duniya kana wasu 153 ake tsare da su a gidajen kurkuku saboda aikinsu.KasaShen China da Masar da Iran na daga cikin ƙasashen da ake tsare da 'yan jaridu da dama a gidajen kurkuku.Nan gaba ne da a ƙarshen wannan wata ƙungiyar za ta fitar da wani rahoto na musammun na addadin 'yan jaridar da aka kashe a duniya a kan aikinsu.