′Yan gudun hijirar arewacin Najeriya na komawa ga matsugunansu | Labarai | DW | 23.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan gudun hijirar arewacin Najeriya na komawa ga matsugunansu

Dubban 'yan gudun hijira na arewacin Najeriya da suka tsira zuwa kasar Kamarun bayan da 'yan boko Haram suka kame garuruwansu na ci gaba da komawa gidajansu.

A cewar daya daga cikin hukumomin birnin na Gamboru Ngala da bai so a bayyana sunansa ba, 'yan watanni uku na baya-bayan nan dai an samu akalla 'yan gudun hijira dubu 15 da suka ketara wannan gada da ta raba garin Gamboru Ngala da Fatokol na kasar Kamarun, inda ya ce a halin yanzu suna da yawan 'yan gudun hijirar da ke ci gaba da dawowa matsugunansu.

'Yan kunguiyar Boko Haram dai sun hallaka mutane fiye da dubu 17 a yankin arewacin Najeriya yayin da wasu fiye da miliyan biyu da rabi suka guje wa matsugunansu tun daga shekara ta 2009.