1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira za su yi zabe a Najeriya

Yusuf BalaDecember 16, 2014

Hukumar zabe a kasar ta Najeriya ta bayyana cewa ayi zabe ba tare da 'yan gudun hijira ba, zai zama mara adalci a cikinsa. Kasancewar su ma 'yan kasa ne da suke da Hakki.

https://p.dw.com/p/1E5qe
Hoto: CC BY-SA 2.0

Majalisar dattawan Najeriya ta cimma wata matsaya da za ta ba wa mutanen da suka tsinci kansu a yanayi na gudun hijira dake warwatse a fadin kasar su yi rejista tare da kada kuri'arsu a duk inda suke. Wani abu da ake ganin zai bude kofa garesu a zabukan kasar dake tafe.

A cewar wata cibiyar nazarin kan 'yan gudun hijira ta kasar Norway, sama da mutane miliyan uku ne 'yan Najeriya suka watsu a wasu sassa daban-daban na kasar. Mafi akasarisu sun fito daga jihohin dake Arewa maso gabashin kasar ta Najeriya inda ayyukan Boko Haram suka addaba tun daga shekarar 2009.

Wannan mataki na majalisar dattawan kasar na zuwa ne kwana daya bayan da hukumar zabe a kasar ta bayyana cewa ayi zabe ba tare da 'yan gudun hijira ba zai zama mara adalci a cikinsa.