′Yan gudun hijira sun tsere daga Maiduguri | Siyasa | DW | 15.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan gudun hijira sun tsere daga Maiduguri

Wasu daga cikin 'yan gudun hijira da ke birnin Maiduguri na Jihar Barno a Najeriya sun yanke matakin komawa inda suka fito da kafa saboda yanayin da suka samu kansu.

Wasu 'yan gudun hijira a Maiduguri sun zabi su tsere daga sansanonin su zuwa garuruwan su da kafa saboda abinda suka bayyana da cewa tsananin wahala da su ke ciki na yunwa saboda rashin abinci da kuma rashin matsuguni.

Wadan nan 'yan gudun hijira na cikin wadanda ruwan sama ya lalata musu matsuguni inda suke cewa ci gaba da zaman su barazana ce ga rayuwarsu. A cewar su gwamnati ta yi alkawarin mayar da su garuruwan su a karshen watan Mayu amma kuma sai suka ji an fasa, shi ya sa suka yanke shawarar tafiya da kafa zuwa garuruwan duk hadurra da hanyoyin garuruwan ke ciki.

Gwamnati da jami'an tsaro dai sun ce akwai sauran ayyukan da jami'an tsaro ke yi a irin wadan nan yankuna shi ne ya sa aka jinkirta komawa ga 'yan gudun hijira.

Sauti da bidiyo akan labarin