1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira sun ga ta kansu a Kamaru

Yusuf Bala Nayaya
September 27, 2017

Kungiyar Human Rights Watch ta ce 'yan Najeriya da suka nemi mafaka a Kamaru bayan tsallaka iyaka sun fiskanci tozartawa ko cin zarafi da ma aikata lalata da wasu a hannun sojoji.

https://p.dw.com/p/2koUv
Symbolbild zur Nachricht - Streitkräfte in Kamerun zerschlagen Boko-Haram-Schule
Hoto: Getty Images/Afp/Reinnier Kaze

An zargi mahukuntan kasar Kamaru da sanya hannu wajen tilasta 'yan gudun hijira 100,000 komawa kasarsu ta Najeriya inda suka kauracewa rikicin Boko Haram, lamarin da ya jefa rayuwarsu cikin hatsari. A cewar 'yan fafutikar hakan ya sabawa dokar kasa da kasa.

Kungiyar Human Rights Watch ta ce 'yan Najeriya da suka nemi mafaka a Kamaru bayan tsallaka iyaka sun fiskanci tozartawa ko cin zarafi da ma aikata lalata da wasu a hannun sojoji. Ta ce wadanda kuma suka samu kansu a sansanin na 'yan gudun hijira na cikin masifa ga rashin tsafta an hansu motsawa, ko ma yin magana da jami'an Majalisar Dinkin Duniya.

Rahoton na Human Rights Watch ya ce tun daga shekarar 2015 a kalla 'yan  gudun hijira 100,000 ne aka mayar da su inda ake fama da tashin hankali a iyakar kasashen na Kamaru da Najeriya. A lokacin mayar da 'yan gudun hijirar ana samun soja na amfani da karfi da ya wuce kima kan mutanen da ke neman tallafi.