′Yan gudun hijira sun fara isa kasar Kwuroshiya bayan Hangari ta rufe iyaka | Labarai | DW | 16.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan gudun hijira sun fara isa kasar Kwuroshiya bayan Hangari ta rufe iyaka

'Yan gudun hijira da a halin yanzu ke kara kwarara kasashen Turai, za su lakume makudan kudaden Jamus, yayin da ake neman mafita kan matsalar tsakanin kasashen Turai.

Kawo yanzu 'yan gudun hijira da bakin haure da dama suka samu isa kasar Kwuroshiya daga Sabiya a wannan Laraba, bayan kasar Hangari ta rufe kan iyaka. Galibin wadanda suka tsallaka iyakar sun fito daga kasashen Siriya da Afghanistan.

Karkashin sabbin dokokin da aka fara aiki da su duk bakon haure da shiga kasar Hangari ba tare izini ba zai fuskanci tuhuma da dauri a gidan fursuna. Kafin fara aiki da dokar kimanin bakin haure 200,000 suka wuce ta kasar ta Hangari domin kai wa zuwa kasashen Turai masu karfin tattalin arziki kamar Ostiriya da Jamus da kuma Sweden cikin wannan shekara. Firaminista Zoran Milanovic na Kwuroshiya ya tabbatar da cewa kimanin baki 150 suka shiga kasar a wannan Laraba kuma kasar za ta iya taimaka musu domin wucewa bisa dalilan jinkai.