1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yan Gambiya da dama sun mutu a yakin Ukraine

February 21, 2026

Gambiya ta bi sahun kasashen Afirka wajen nuna damuwarta kan yadda matasan nahiyar ke rububin shiga aikin soja a Rasha.

https://p.dw.com/p/59BFd
Sojojin Najeriya da ke samun horo daga sojojin kasashen waje
Sojojin Najeriya da ke samun horo daga sojojin kasashen wajeHoto: James Sheehan/U.S. Army/REUTERS

Kafofin yada labarai da dama ciki har da wani rahoto na kamfanin dillancin labarai na AFP wallafa, sun bayyana yadda hukumomin Rasha ke daukar matasa da sunan aiki, wanda daga bisani suke karewa a filin gwabza yaki tsakanin Rashar da Ukraine.

Karin bayani:Afirka ta Kudu ta nemi dawo da mutanenta da ke yakin Rasha

Ma'aikatar yada labaran Gambiya ta sanar da cewa ta samu rahotannin mutuwar 'yan kasarta da dama a yakin Ukraine, duk da cewa hukumomin Banjul ba su bada adadin 'yan kasar da suka rasa rayukansu a yakin Ukraine ba. Gwamnatin Gambiya ta bukaci daukacin al'ummar kasar da su kauracewa zuwa kasashen ketare domin shiga aikin soja.

Karin bayani:Rasha tana saka 'yan Afirka a yaki da Ukraine

A wata sanarwa da Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Andriy Sybiga, ya fitar a watan Nuwambar 2025, ya ce akwai 'yan kasashen nahiyar Afirka akalla 1,436 daga kasashe 39 na Afirka da ke cikin kunshin sojojin Rasha.