′Yan fashin teku sun sace Turkawa 15 | Labarai | DW | 24.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan fashin teku sun sace Turkawa 15

'Yan fashi da makami a teku sun kashe Baturke ma'aikacin jirgin ruwan Turkiyya daya, tare da yin garkuwa da ma'aikatan jirgin 15 lokakacin da jirgin ruwan ya tashi daga Lagas zai nufi birnin Cape Town na Afirka ta Kudu.

Hukumomin kula da jiragen ruwan Turkkiyya sun ce ma'aikatan jirgin sun killace kansu a boyayyen wuri amma sai dai 'yan fashin suka balla wurin bayan kwashe sa'a shida suna fama, barayin sun bar jirgin a tekun Guinea da wasu ma'aikatan jirgin uku a cewa kafanin yada labaran Turkiyya Anadolou.

Gabar tekun Guinea da na Najeriya da Togo da Benin da Kamaru, na su ne gabar teku mafi hatsari na 'yan fashi a duniya a cerwa hukumar kula da teku na kasa da kasa. Ko a 2019, sai dai 'yan fashin tekun Najeriya suka yi garkuwa da Turkawa 10.