'Yan daba sun bude fursunoni a Legas | NRS-Import | DW | 22.10.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

'Yan daba sun bude fursunoni a Legas

Masu tarazoma sun kai hari a gidan yarin da ke Ikoyi a Legas, fursunoni da dama sun gudu. Jami'an tsaro sun je wurin bayan harin.

Mazauna kusa da yankin Ikoyi sun ji karar harbin bindigogi yayin da ake ganin tirnikewar hayaki ta gidan yarin da ke yankin. Shaidu sun tabbatar wa kamfanin dillancin laraban reuters ganin motocin 'yan sanda biyu cike da jami'an tsaro sun nufi gidan yarin.

Jihar Legas da ke zaman cibiyar kasuwacin Najeriyar na da yawan mutane miliyan 20, jihar na cikin dokar hana fita tun bayan zanga-zangar kawo karshen 'yan sandan Sars da ta rikede zuwa tarzoma. Akwai dai karin wasu jihohi biyar da ke cikin irin doka domin takaita tashin hankali, yayin da jihar Delta ta ce za ta sanya dokar hana fita na tsawon kwanaki biyu daga karfe shida.