′Yan ci-rani a Jamus sun soki manufofin jam′iyyar SPD | Siyasa | DW | 13.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan ci-rani a Jamus sun soki manufofin jam'iyyar SPD

Wakilan jam'iyyar SPD masu asali daga ƙetare sun bayyana rashin jin daɗi kan manufiofin jam'iyyar game da matsayin baƙi masu paspo na ƙasashe biyu.

Jam'iyyar Social Democrats, wato SPD a nan Jamus tayi iyakacin ƙoƙarinta wajen jan hankalin magoya bayanta game da samun amincewar su ga yarjejeniyar kafa gwamnatin haɗin gwiwa a tarayya da ta cimma da jam'iyyar CDU To sai dai ko da shi ke ana sa ran jam'iyyar zata sami wannan amince wa, amma ana kuma samun masu sukan wasu daga cikin manufofinta. 'Yan siyasar jam'iyyar ta SPD a fannin kula da yan ci-rani, sun nuna fushi game da manufofinta kan baƙi masu riƙe da paspo na ƙasashe biyu.

Ni a gare ni, yarjejeniyar ta kafa gwamnatin haɗin gwiwa ta tarraya mummuna kaye ne ga tsarin Social Democrats, inji Ali Dogan, wanda bai ɓoye komai ba game da yadda ra'ayinsa yake tattare da wannan yarjejeniya. Dogan, mataimakin shugaban jam'iyyar SPD na ƙasa mai kula da ma'aikata baki, ya ce shugabannin jam'iyyarsa sun bashi kunya matuƙa. Yace yana iya tuna cewar a lokacin babban taron jam'iyyar a tsakiyar watan Nuwamba, shugabanta yace ɗaya daga cikin manyan buƙatun da za ta matsa lamba kansu shi ne, idan ba tare da an bai wa baƙi yan ci-rani izinin riƙe paspo na ƙasashe biyu ba, to kuwa SPD ba za ta amince da ko wacce irin yarjejeniya ba. To amma sai ga shi cikin dare ɗaya wannan buƙata ta ɓace.

Mahawara na ƙara yin zafi a cikin jam'iyyar ta SPD dangane da batun yarjejeniyar

Große Koalition CDU und SPD einigen sich 27. Nov. 2013 Koalitionsvertrag

Shugaban SPD Sigmar Gabriel da shugaban jam'iyyar CDU Angela Merkel

A ƙarshen watan Nuwamba shugabannin jam'iyyun SPD da CDU suka gabatar da tsarin abubuwan da ke ƙunshe a yarjejeniyar ta gwamnatin haɗin gwiwa a bainar jama'a. Ɗaya daga cikin al'amuran da suka haddasa muhawara shi ne batun bai wa baƙin damar riƙe paspo na Jamus da na ƙasashen su na asali a lokaci guda. Ƙarkashin dokar da ke aiki yanzu, 'ya'yan baƙi da aka haifesu a nan Jamus kuma suke da paspo na Jamus, tilas kafin su cika shekaru 23 da haihuwa su yanke ƙudirin paspo daya da za su riƙe. Idan suka wuce wannan lokaci ba su yanke shawara ba, suna iya fuskantar barazanar ƙwace masu paspo na Jamus. Yanzu dai wannan ɓangare na dokar an kawar da shi. Sulhu da aka cimma tsakanin jam'iyyun ya tanadi cewar 'ya'yan baƙi suna iya rike paspo biyu, to amma wannan sassauci ba zai shafi yaran da aka haifesu a ƙetare aka shigo dasu nan Jamus ba. Wannan ɓangare musamman ya shafi Turkawa ne da suka shigo nan Jamus a shekaru na 50 da na 60 a matsayin yan ci rani. Dangane da haka ne Ali Dogan ya ce.

Baƙi na yin tsokaci a kan tsarin jam'iyyar a kan maganar paspo

''Kamar yadda Turkawa suke kallon al'amarin, yarjejeniyar ta kafa gwamnatin haɗin gwiwa, a fannin manufofin baƙi da zamantakewarsu a Jamus mummunan kuma baya ce kuma kuskure, saboda ta shafi mutane ne masu ra'ayoyi da al'adu da suka banbanta da juna wadanda a bangarori da yawa suka ƙasa samun haɗin kai.'' Ali Dogan ya ƙara da cewar

Ali Dogan

Shugaban bangaren ma'aikata na jam'iyar SPD Ali Dogan

'' Bai kamata jam'iyar SPD ta ɗauki matakin da zai zama kamar dai yi wa baƙi yan ci rani kora-da-hali ba ne, saboda baƙi da ke da asalinsu a ƙetare, suna da matuƙar muhimmanci a matsayin masu zaɓe a Jamus, inda a lokacin zaɓen majalisar tarraya da aka yi a watan Satumba, baƙi misalin miiyan huɗu ne suka kaɗa kuri'unsu, fiye da rabi suka zaɓi jam'iyyar SPD.''

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi:Daniel Heinrich/Umaru Aliyu
Edita: Abdourahamane Haassane

Sauti da bidiyo akan labarin