′Yan Boko Haram sun ƙaryata mutuwar Shekau | Labarai | DW | 02.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan Boko Haram sun ƙaryata mutuwar Shekau

Shugaban Boko Haram, ya sake bayyana a wani sabon faye-fayan bidiyo inda ya ce yana nan da ransa, bayan kuma da sojojin wannan ƙasa suka sanar da mutuwarsa.

Wannan mai magana da a ka ce Abubakar Shekau ne, ya ƙaryata batun da sojojin Najeriya su ka yi na cewar sun samu nasarori da dama a kansu, inda ya tabbatar da kafa Shari'ar muslunci a yankunan da ke hannunsu, tare da kiran kansa Khalifan Islama na Arewa maso gabacin Najeriya. A cikin bayanin da yayi, yana mai cewar, ga shi da ransa, kuma zai mutu ne amma sai lokacin da Allah ya ɗauke rayuwarsa, sannan kuma ya ce, Ƙungiyar ta Boko Haram za ta ci gaba da zartas da shari'ar muslunci a yankunan da take jagoranta.Dama dai ƙasar Amirka, da ma sauran ƙwararru, sun nuna ƙonƙontonsu kan sanarwar da sojojin na Najeriya suka fitar ta cewa sun kashe shugaban na boko haram.