′Yan bindiga sun kashe mutane a jihar Borno | Labarai | DW | 27.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun kashe mutane a jihar Borno

Akalla mutane 14 ne suka gamu da ajalinsu, sakamakon dirar mikiya da wasu da ake zato 'yan Boko Haram ne suka yi wa garin Kimba da ke Gabashin jihar Borno a Najeriya.

Wannan majiya ta mayakan sa kai da ke mara wa dakarun gwamnati baya a yakin da suke da kungiyar ta Boko Haram, ta sanar cewa bayan ma kashe mutanen 14 mayakan sun kone illahirin gidaje da ke cikin wannan gari bayan da suka shigeshi a wajajen karfe 10 na dare tare da bude wuta kan jama'a kafin daga bisani su tsere.

Rahotanni na cewa akasarin wadanda suka samu tsira da rayukansu, sun isa garin Biu inda aka shigar da su a sansanin 'yan gudun hijira wanda tuni ya cika da jama'a. Sai dai kuma masu lura da al'amura na ganin cewa ayyukan na Boko Haram a halin yanzu wani shure-shure ne wanda bayya hana mutuwa.