′Yan awaren Ukraine sun gudanar da Zaɓen raba gardama | Siyasa | DW | 12.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan awaren Ukraine sun gudanar da Zaɓen raba gardama

Ko da shi ke hukumomin yankunan sun yaba da zaɓen amma rahotannin na tabbatar da cewar an samu ƙarancin kayayyakin aiki.

Zaɓen raba gardama da 'yan awaren Ukraine suka gudanar a yankunan Donetsk da Louhansk da ke gabashin ƙasar, ya samu amincewar mafi yawan mutanen yankin da kashi a ƙalla 89 cikin ɗari, a cewar hukumomin da ke goyon bayan Rasha. Dama dai tun a watan Afrilu ne 'yan awaren na Ukraine masu goyon bayan Rasha suka ayyana yankin na Donetsk a matsayin Jamhuriyar Donetsk. Bisa takardun zaɓen dai an tambayi masu zaɓen ne, har suna iya ba da goyon bayan su wajen mayar da Donetsk ƙasa mai yanci,wannan matar na daga cikin waɗanda suka kaɗa ƙuri'a

An samu amincewa da babban rinjaye

''Muna gagwarmayya ne domin ƙwato wa kanmu ‘yanci daga ƙasashen yamma da ke neman cusa mana ra'ayi. Mun tashi tsaye domin samar wa kanmu ‘yancin faɗan albarkacin baki da kuma samar wa yankinmu makoma ta gari. Harshuna daban- daban ake amfani da su a wannan yanki, lamarin da ƙasashen yamma ba sa la'akari da shi.''

Tuni dai a safiyar wannan Litinin din (12.05.2014) a ka yi ta jin ƙaran wasu manyan makammai da fashewar wasu bama-bamai a cikin wasu yankunan na gashin Ukraine ɗin

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin