′Yan aware sun harbo jirgin yakin Ukraine | Labarai | DW | 29.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan aware sun harbo jirgin yakin Ukraine

'Yan aware a gabashin Ukraine sun harbo wani jirgin yakin kasar da ke dauke da dakarun kasar 14 ciki kuwa har da wani Janar.

Ukraine Gewalt Slawjansk 05.05.2014

'Yan awaren Ukraine cikin motar yaki mai sulke

Shugaban Ukraine din na rikon kwarya Oleksandr Turchynov wanda ya tabbatar da mutuwar sojin da ke cikin jirgin, ya shaidawa majalisar dokokin kasar dazu cewar 'yan awaren sun harbo jirgin ne kusa da yankin nan na Slavyansk kuma sun yi amfani ne da makami kirar Rasha.

Gabannin wannan jawabi na Mr. Turchynov dai, wani mai magana da yawun 'yan awaren ya shaidawa kafafen watsa labarai a kasar Rasha cewar sun harbo jirgin sojin Ukraine mai saukar ungulu yayin da suke dauki ba dadi da dakarun Ukraine din a wani yanki da suke rike da shi. Mutumin wanda bai ambaci sunansa ba ya kuma ce sakamakon taho mu gama din da suka yi da dakarun na Ukraine, gidajen fararen hula da dama da ke yankin sun kone.

Wannan rashin da Ukraine din ta samu na sojinta dai shi ne kusan mafi muni da ta fuskanta tun bayan da 'yan aware suka fara tada kayar baya a gasbashin kasar cikin farkon watan Afrilun da ya gabata.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu