′Yan adawar Siriya za su halarci taron zaman lafiya na gaba | Labarai | DW | 10.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawar Siriya za su halarci taron zaman lafiya na gaba

Amma masu kokarin ganin bayan shugaba Bashar al-Assad sun ce dole sai Rasha ta daina kai farmaki a kan wurarensu.

'Yan adawa da shugaba Bashar al-Assad na kasar Siriya da ke samun tallafin kasar Saudiyya sun ce za su halarci taron neman zaman lafiyar kasar da aka shirya gudanarwa karshen wannan wata, sannan a lokaci guda sun yi kira ga Amirka da ta tashi tsaye ta tilasta wa Rasha ta dakatar da ruwan bama-baman da take yi kan wuraren 'yan adawa. Salim Al-Muslat da ke zama kakakin 'yan adawar ya yi wannann furucin yana mai cewa.

"E za mu tafi, za mu kuma ga taron yayi nasara. Sai dai ba mu da tsayayyen abokin tattaunawa. Ina ganin idan za ka nemi sasantawa ta siyasa, kana bukatar ka nuna wani abu a kasa. Idan suka daina kashe 'yan Siriya, na yi imani za a samu wata matsaya a taron."

Sai dai kuma al-Muslat ya fada wa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa za su halarci taron ne idan suka ga an tura wa yara a Siriya da abinci sannan Rasha ta daina yi musu ruwan bama-bamai.