1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tanadin shari'a kan mayakan sa-kai a Ukraine

Ramatu Garba Baba
March 14, 2022

Dubban mayakan sa-kai da suka shiga yakin Rasha da Ukraine don taimaka wa Ukraine kare kanta daga mamayar Rasha ka iya fuskantar sakamako na shari'a a nan gaba.

https://p.dw.com/p/48Qkr
Deutschland | Bundeswehr Übungsgelände in Münster
Hoto: Sean Gallup/Getty Images

Wani bincike ya gano cewa, dubban mayakan sa-kai da suka shiga yakin Rasha da Ukraine a kokarin gwamnatin Kyiv na kare kanta daga mamayar Rasha ka iya fuskantar sakamako na shari'a idan sun koma kasashensu nan gaba.

Daga cikin wadanda wannan doka za ta iya yin tasiri akan su, sun hada da 'yan asalin kasashen Britaniya da Australiya a yayin da Jamus da Kanada da Denmark suka ce, ba za su dauki ko wani matakin shari'a kan wadanda suka taimaka ma Ukraine ba.

Wannan na zuwa ne a yayin da aka soma nazarin abin da ka iya biyo bayan fadan da ake zargin an tafka laifukan yaki a cikinsa, inda ake tunanin gurfanar da wadanda ake zargin suna da hannu a laifukan a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya domin yi musu shari'a dama yanke musu hukunci.

A daya bangaren kuwa, Andrei Melnichenko, wani fitaccen attajirin kasar Rasha ya ce, dole ne a gaggauta kawo karshen yakin Rasha da Ukraine ko kuma duniya ta fuskanci matsala ta matsananciyar yunwa. Attajirin ya ce, manoma sun fara fuskantar matsala saboda tsadar taki na amfani a gonakinsu, lamarin da ya danganta da alamu na barazanar karancin abinci.

Ita kuwa Rasha na ci gaba da matsa kaimi a mamayar makwabciyarta, fadar Kremlin ta nemi taimakon sojoji daga Chaina dama tallafin inganta tattalin arzikinta, sai dai tuni Amirka ta gargadi Chaina bayan da ta ce, za ta fuskanci munanan sakamako, muddun ta amince da bukatar Rasha. An shiga mako na uku da soma yakin inda rikicin ya tilasta wa mutum fiye da miliyan biyu tsere wa gidajensu a Ukraine.