Yaki ya sa bazuwar makamai a Gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 12.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaki ya sa bazuwar makamai a Gabas ta tsakiya

Cibiyar SIPRI mai bincike kan sayar da makamai a duniya, ya zargin Amirka da sauran kasashen Turai ciki harda Jamus wajen shigar da makaman yaki zuwa kasashen Gabas ta tsakiya fiye da kima a shekarun baya-bayannan.

Adadin makamai da kasashen duniya ke shigo da su yankin Gabas ta tsakiya ya karu da kashi 103 a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2017. Rahoton na SIPRI ya nuna kasar Saudiyya na kan gaba wajen shigo da makamai a kasar Yemen, sakamakon yaki da take yi da 'yan tawayen Houthi.

Amirka ta kasance kasar da tafi kowace yawan fitar da makamai a shekaru biyar da suka gabata, inda aka zargeta da sayar da mafi yawan makamai da ake yaki da su a kasahen Gabas ta tsakiya.