1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki ya ki ci ya ki cinyewa a Afirka ta Tsakiya

February 13, 2014

Duk da kokarin da ake na wanzar da zaman lafiya, har yanzu ana ci gaba da yi wa wani bangare na al'ummar Afirka ta Tsakiya kisan kare dangi.

https://p.dw.com/p/1B7za
Zentralafrikanische Republik Sangaris-Soldaten Polizist 09.02.2014
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Kisan kai da kwasar ganima, su ne manyan matsalolin da 'yan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ke fuskanta kama daga babban birnin ƙasar wato Bangui zuwa sassa daban daban na ƙasar. Duk kuwa da sojojin ƙasashen wajen dake ƙasar bai hana al'ummarta shiga cikin halin ha-ula'i ba inda ko a cikin farkon watan Fabrairun nan al'ummar dake zaune a ƙauyen Nzakun dake da iyaka da ƙasar Cadi ta fuskanci muguwar ta'asa ta kisan gilla.