1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin warware rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Umaru AliyuJanuary 9, 2014

Shugabannin ƙasashen yankin tsakiya na Afirka na gudanar da taro a Chadi da nufin samar da hanyoyin kawo ƙarshen tashin hankali Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a dai dai lokacin da manazarta ke cewar Faransa ta gaza.

https://p.dw.com/p/1Annl
Zentralafrikanische Republik Vereidigung Michel Djotodia
Hoto: STR/AFP/Getty Images

Wata guda bayan da Faransa ta aike da dakarunta a jamhuriyar Afirka taTsakiya da nufin dakatar da abin ka iya zama bala'i ga ƙasar. Har yanzu tsugune ba ta kare ba a ƙasar inda kusan mutane miliyan biyar suka ficewa faɗan da ake yi,yayin da wasu da dama suka rasa rayukansu. Masu yin nazari a kan al'amura dai na cewar tawagar sojojin Faransa a jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya ba ta gyara komai ba, abin da ya sa ake ganin cewar babu wata nasara da suka cimma. Ulrich Delius shi ne shugaban wata ƙungiyar ta ƙasar Jamus da ke fafutkar kare hakin bil adama da kuma tsiraru masu fuskantar barazana, kana kuma masanin nahiyar Afirka, Ya ce '' mun yi la'akari da cewar tun lokacin da sojojin Faransa suka fara kai ɗauki a ƙasar,yawan 'yan gudun hijira ya ƙaru, hakan na nuna cewar abubuwan ba sa tafiya da kyau.''

Al'ummar Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya na fuskantar barazana

Tun da farko MDD ta ce kusan kishi ɗaya bisa huɗu na yawan al' ummar ta Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun fice daga ƙasar kusan mutun miliyan biyar, yayin da sauran al'ummar ƙasar ke yin rayuwa cikin wani hali na damuwa da ɗimuwa na hare- hare da fyaɗe da ake kai musu ba dare ba rana. A cikin watan Disamba na shekarar da ta gabata ne Faransa ta aike da dakaru 1200 a Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya bayan umarni da shugaba Francois Hollande ya bayar da kuma wasu ƙarin sojojin na ƙasashen Afirka 3500 na rundunar kiyayen zaman lafiya ta MDD.

Zentralafrikanische Republik Trinkwasser in Bangui 07.01.2014
Ƙarancin ruwan sha na pompi a Bangui.Hoto: picture-alliance/AP Photo

Ƙarancin sojojin Faransa a ƙasar shi ne ya janyo cikas

Tashin hankalin wanda ya biyo bayan faɗuwar gwamnatin Francois Bozize wanda jagoran tsohuwar ƙungiyar 'yan tawayen ta SELEKA Michele Djotodia ya kifar da gwamnatinsa a cikin wata Maris na shekara bara. Babu wanda ya yi tsamani zai rikiɗe ya koma yaƙin ƙabilanci da addini, a cikin ɗan lokaci ƙanƙane mutane kusan dubu suka rasa rayukansu a cikin wata guda. Jean Claude Francois Allard shugaban wata cibiya da ke yin nazarin a kan hulɗa ta ƙasa da ƙasa ya ce rashin isassun sojojin na Faransa a Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa aka gaza samu nasara. Ya ce : '' Ta ƙaƙa za a iya cewar birnin na Bangui mai yawan al' umma kusan miliyan ɗaya 'yan sanda dubu ɗaya da ɗari shida kawai zasu iya kula da tsaron birnin.''

Zentralafrikanische Republik Frankreich Sangaris Gespräch in Bangui 06.01.2014
Kwamanda Thomas Mollard jagoran bataliyar sojojin Faransa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.Hoto: picture-alliance/AP Photo

Rashin adalci sojojin Faransa a kan ɓangarorin da ke gaba da juna

Kuskuran da sojojin Faransa suka aikata shi ne na kwance ɗamarar musulumi tsirarru abin da ya bai wa mayaƙan sa kai na Kirista waɗanda ake kira da sunan Antibalaka damar kai hare-hare a kan musulumi. Abin da ya ƙara dagula al'amura a birnin Bangi da sauran biranen wanda kuma ya zama cikas ga wasu ƙungiyoyin agaji wajen kai ɗauki ga jama'ar da ke cikin sansanonin 'yan gudun hijira waɗanda ke buƙatar agajin gaggawa a cewar Ulrich Delius.Ya ce : ''Da kaɗan-Kaɗan da ƙer ake iya samun ƙungiyoyin da ka iya zuwa su yi aiki a cikin irin wannan hali na aikin asha da ake aikatawa a ƙasar. Abin da muke yin Allah Wadai da shi shi ne fatali da ƙasashen duniya suka yi da halin da ake cikin a jamhuriyar ta Afrika ta Tsakiya, kuma idan ka duba tashin hankali da ake yi a Sudan ta Kudu ya fi daukar hankali kasashen duniyar fiye da na Afirka ta Tsakiya.

Französische Armee in Zentralafrika
Sojojin Faransa a Bangui

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto da rahoton da wakilanmu na Kano Nasiru Salisu Zango da kuma Larwana Malam Hami na Zinder suka aiko mana a kan yan gudun hijirar daga Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya wɗanda suka dawo gida.

Mawallafi : Borowski / Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh