1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsugunne bata ƙare ba a Afirka ta Tsakiya

February 12, 2014

Duk da dakarun ƙetaren da aka kai Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin taimakawa wajen kawo sauƙin rikicin addinin da ya ɓarke a ƙasar, lamarin na barazanar rikiɗa zuwa kissan kiyashi

https://p.dw.com/p/1B7dd
Zentral Afrikanische Republik UN Truppen nach Bangui
Hoto: PACOME PABANDJI/AFP/Getty Images

Kisan kai da kwasar ganima, su ne manyan matsalolin da 'yan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ke fuskanta kama daga babban birnin ƙasar wato Bangui zuwa sassa daban daban na ƙasar. Duk kuwa da sojojin ƙasashen wajen dake ƙasar bai hana al'ummar wanan garin shiga cikin halin ha-ula'i ba inda ko a cikin farkon watan nan al'ummar dake zaune a ƙauyen Nzakun dake da iyaka da ƙasar Chadi ta fuskanci muguwar ta'asa ta kisan gilla.

Wannan ta'asa ta faru ne a daren 4 ga watan Febrairu inda shaidun gani da ido suka faɗa cewa kashe-kashen da aka yi a wannan ƙauyen na Nzakun ya yi muni ƙwarai da gaske.

Wani jami'in diplomasiya da ke a ƙauyen Ngaoundaye dake maƙwabtaka da ƙauyen Nzakon wanda ya yi tattaki zuwa inda abun ya faru ya nemi da a sakaye sunansa yana mai cewa.

"Na ga gidaje uku, na farkon akwai mutun 6 wadanda suka mutu a cikin na biyu ma haka naga mutun 5 a cikin na uku akwai mutun 3 kuma duk sun mutu. wannan ai kisan kiashi ne."

A cewar jami'in diplomasiyan mutane 20 suka mutu a cikin tashe- tashen hankali da ƙone-ƙonen gidaje da kuma satar ganimar jama'a. Wannan ya sanya mazauna ƙauyen barin matsugunensu zuwa daji.

A cewar malamin cocin babu watatantama tsofin 'yan tawayen ƙungiyar seleka suka aikata wannan ɗanean aikin, saboda a cewar shi ya na da shaida ta wasikar da suka aika cewa za su zo, kuma sai sun biya taƙauyen Ngaoudaye kafin su wuce zuwa kasar Chadi.

'Yan Seleka sun zo a Nzakoun, sun kwana biyu a can, a ranar Talata suka rubuta wasikar da suka aika a ƙauyen mu na Ngaoudaye. Ina da tabbacin su suka aikata wannan ta'asar saboda bayan sun aika wasikar, waɗanan motocin su da baburansu suka wuce daga ƙauyenmu inda a hanyar wucewansu suka ƙona mana gidaje 6.

Duk da rashin tsaron da ƙasar ke fuskanta malaman coci b asu yarda da a kwashesu ba. Tashe-tashen hankula a Jamburiyar Afrika ta Tsakiya da keda mutane milyan 6 ta zama sanadiyar tserewar mutane kusan milyan daya zuwa gudun hijira.

Mawallafiya: Ramatu Issa

Edita: Pinaɗo Abdu Waba