Ci gaba da zaman fargaba a Afirka ta Tsakiya | Siyasa | DW | 27.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ci gaba da zaman fargaba a Afirka ta Tsakiya

Duk da zaɓen shugabar gwamnatin riƙo da kuma firaministan ƙasar kwanciyar hankali ba ta dawo ba a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ba.

Yanzu haka al'umma a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na zaman jiran ganin an naɗa sabbin manbobin majalisar ministocin ƙasar bayan da shugabar ƙasar ta wuccin gadi ta naɗa firaminista a ƙarshen mako a yayin da aka shirya gobe Talata kwamitin sulhu na MDD zai amince da wani daftarin ƙudiri na ɗaukar matakan hukunta waɗanda ke da alhaki tayar da fitina a ƙasar. Hukuncin da MDD za ta yanke zai shafi waɗanda suka yi ruwa suka yi tsaki wajen kawo cikas ga hanna ruwa gudana a al' ammuran gwamnatin wuccin gadin ta hanyar haddasa tashin hankai da ya janyo kisan dubban jama'a da kwasar ganima a shagunan jama'a tare da take hakin bil addama da kuma dokokin na ƙasa da ƙasa.

Sabon firaministan ya sha alwashin tabbatar da zaman lafiya

Ko da shi ke sabon firaministan da aka naɗa wato André Nzapayeké, da shugabar wuccin gadin Catherine Samba Panza sun yi alƙawarin dawo da doka da oda tare a tattaunawa da dukkannin ɓangarorin da ke gaba da juna domin samar da zaman lafiya har yanzu da sauran aiki. Ɗaya daga cikin shugabannin Ƙungiyar Antibalaka mista Felix ya ce suna da buƙatu. Ya ce : ''Ba zamu ajiye makamai ba haka nan kawai yakamata mu tattauna da shugabar ƙasa mu gabatar mata da buƙatun da muke da su ,ta haka kawai na ke ganin za a samu kwanciyar hankali kuma zamu iya ajiye makamai mu goyi bayanta domin samar da zaman lafiya a ƙasarmu.''

SELEKA ta ce ba ta da alhakin kai hare-haren

Musulmai dai marasa rinjaye a ƙasar na ci gaba da kasancewa cikin fargaba da kuma rashin sanin tabbas du kuwa da zaɓen sabuwar shugabar ƙasar da firaminista an ci gaba da kai hare hare a tsakiyar birnin Bangui. Kuma yanzu haka wani jami'in Ƙungiyar Human Rights Watch Peter Bouckaert ya sanar da cewar mayaƙan ƙungiyar 'yan tawayen na SELEKA sun fara ficewa daga birnin Bangui zuwa garin Bossembele da ke a yankin arewaci, domin ganin an kwantar da wutar rikicin da ke ƙara rurruwa, sai dai wani jami'in Ƙungiyar SELEKA ya ce ko can daman ba su da alhakin kai hare-haren. Ya ce: ''An ce mu dukkanin dakarun SELEKA mu koma cikin rundunonin mu tun daga wannan lokaci kawo yanzu babu wani ɗan SELEKA da ke yin yawo da bindiga a cikin gari, duk hare-haren 'yan Antibalaka ne ke kai su, sune ke ƙone gidajen tsofin mayaƙan ƙungiyar SELEKA da musulmai, yawancin 'yan Antibalaka sojoji ne da 'yan sanda.''

Ta kowane ɓangare dai sabuwar shugabar ƙasar na fuskantar ƙalubale haka ma da ƙungiyar 'yan adawa ta ƙasar AFDT wacce ta ce ba za ta amince ta shiga a cikin sabuwar gwamnatin riƙon ƙarya ba, saboda tana tsamani yakamata a ce firaminista ya fito ne daga ɓangaranta.'' Nan zuwa wani lokaci ne ake sa ran firaminista zai bayyana sunayen sabbin manbobin majalisar ministiocinsa.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannnan rahoto haɗe da rohoto na musamun na hirar da tashar DW ta yi da shugabar riƙo ta Jamhuriyar Akrika ta Tsakiya Catherine Samba Panza.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Auwal

Sauti da bidiyo akan labarin