Yaki da halasta kudadan haramu a Najeriya | Siyasa | DW | 09.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yaki da halasta kudadan haramu a Najeriya

Hukumar EFCC mai yaki da halasta kudadan haramu ta gurfanar da Raymond Dokpesi da ke a matsayin tsohon shugaban kamfanin labarai na DAAR a Najeriya.

A baya dai ya yi kaurin suna a bisa matsayinsa na Jonathan ko kafar katako, to sai dai kuma yanzu ya bi sahu na ma su siyasa wajen fuskantar barazanar kai wa ya gidan yari a bisa laifukan da suka shafi halasta kudadan haramu. Jerin laifuka dai- dai har guda shida ne dai Raymond Dokpesi, yake shirin amsawa bayan da hukumar ta EFCC ta ce shi da kamfaninsa na DAAR communications sun saba dokar halasta kudin haramun din na kasar ta Najeriya.

Dokpesin da ya amince karbar tsabar kudi har naira Miliyan dubu biyu da dari daya a offishin tsohon mashawarcin tsaron kasar da ma kamfanin DAAR communication da ya kai ga kafa wa can baya, na shirin zama ma su sana’ar ta jaridar na farko a Najeriya da ke iya kare wa a gidan yari a bisa wani laifin da bashi ruwa balle tsaki da batun aiki na jarida. Duk da cewar dai har ya zuwa wannan rana, madugun zarcewar ta Jonathan bai kai ga bayyana a gaban alkali domin tabbatar da amsar laifin nasa ba, sai dai kuma tuni baiyyanar hukuncin ta fara jawo muhawara a tsakanin masu sana’ar ta jarida cikin kasar. A cewar mallam Shu’aib Leman sakataren kungiyar 'yan jaridar kasar ta NUJ, kungiyar bata da bacin rai a bisa kamen Dokpesin da suke zargi da gazawa wajen sauke nauyin tafiyar da kamfanin.

Supreme Court Abuja, Nigeria

To sai dai kuma in har tsallen murna na zaman karatun yan uwa ga jaridar Dokpesi, ga yan uwa na Dalhatu Bafarawa da dansa Sagir da suka share tsawon kusan makonni biyu suna bakuntar EFCC, akwai alamu na siyasa a cikin kamen na su a tunanin mallam Yusuf Dingyadi da ke zaman kakaki na iyalin tsohon gwamnan na Sokoto. Abun jira a gani dai na zaman mafita a tsakanin tsoffafi na jami’an na tsohuwar gwamnatin da ke zaman zakaran gwajin dafi na yaki da cin hanci da wannan sabuwar gwamnati ta sa wa gaba. 

Sauti da bidiyo akan labarin